DUNIYAR COMPUTER a Karama FM 92.1 Kaduna

Alhamdu lillahi! Da haka muka soma kuturu ya ga mai kyasfi, wannan mujalla ta Duniyar Computer ta kasance daya daga cikin shirye-shirye ne da ake gabatarwa a sashen karama FM na Rediyon Najeriya na Kaduna wanda a yau  kimanin watanni bakwa da farawa kenan.

Kwararre kuma daya daga cikin jagororin  wannan mujalla Malam Muhammad Sulaiman  ne ya ke gabatar da shirin a kowace ranar Lahadi tare da babban ma’aikaci kuma kwararre a fannin gabatar da shirin  rediyo Mal. Mustapha Musa Dikwa.

shirin Duniyar Computer a Rediyon Karama FM, ya zamanto wani dandali ne da ke da masu sauraro fiye da dubu dari takwas wanda kuma ake samun tambayoyi daga sassa na jaha baki daya. Shi wannan shiri shine shiri na farko da aka fara gabatar da shi a karkashin wannan mujalla wanda abun ya zo a matsayin gamo da katar. Kasancewar shi Mal. Muhammmad Sulaiman daya ne daga cikin ma’aikatan Digital Computer and Information Services dake Kaduna a matsayin mai lura da sashen gyare-gyare da kuma karantarwa. Alakar dake tsakanin Muhammad Sulaiman da kuma gidan rediyo shine, ya kasance shi ke lura da mafi yawa daga cikin computocin da ma’aikatan gidan suke amfani da su. Wannan dalili ne yasa sashen hausa na bangaren FM suka nemi shi Mal. Muhammad Sulaiman da ya zo ya fara gabatar musu da shiri na musamman wanda zai rinka wayar da kan al’ummar hausawa dama masu jin wannan harshe dangane da abinda ya shafi computer da dangoginta. To da haka muka fara wanna shiri a Karama FM 92.1.

A wannan shiri Muhammad Sulaiman yana amsa tambayoyin masu saurare kuma yana gabatar da  darasi bayan darasi tare da  yin bayani da kuma warware zare da abawa akan abinda ya shafi wannan fanni.  Ana gabatar da wannan shirin ne  ranar Lahadi da misalin karfe 3:00 na rana  zuwa 4:00 na rana a kuma  maimaita shirin a kowace ranar Alhamis daga 9:00 na dare zuwa 10:00 na dare.

Mal. Musatapha Musa Dikwa wanda kusan duk wanda ya kwana ya tashi a garin Kaduna yasan shi kwararren dan Jarida ne mai kama da lauya a wajen iya yin tambaya da kuma neman ayi bayani dalla-dalla, hakika yin wannan shiri da shi ya kara taimakawa wajen fito da shirin da kuma saka shi mai gabatarwar akan hanya madaidaiciya.

Daga karshe makasudin wannan shiri shine domin wayar da kan al’ummar mu ta hausawa da kuma masu jin hausa wajen fahimtar da su zallan ilimin computer da kuma dukkan abin da ya shafi kimiyya da kuma fasaha.

Dukkan wanda yake da wata matsala dangane da Computer kuma yana son al’umma su amfana da tambayar sa wadanda suke cikin garin Kaduna da kewaye zasu iya aiko da sakon wasika zuwa ga wannan lamba 08099604235 sannna kuma wannan lamba ba kira ake yi ba ana aiko da sakon sms ne kawai. Haka kuma za a iya aiko da sakon imel a duniyark@gmail.com.