spot_imgspot_img

Ma’anar harafin ‘i’ da ke cikin iPhone

Muna ganin wannan harafi na ‘i’ tare da dukkan kayan da kamfanin Apple dake kasar Amurka suka kirkiro, an soma ganin wannan harafi tun a shekarar 1998 lokacin da kamfanin ya kirkiro wata computer ya kuma sa mata suna iMac. To mene ne dalilin sa harafin ‘i’? Mene ne ma’anar shi?

Duk da akwai abubuwa na shaci-fadi da yake yawo a intanet game da ma’anar wannan harafi da ake samunsa a jikin kayan apple sai dai gaskiyar abin da wannan harafi ke nufi sau mun koma a shekarar 1998 da aka kaddamar da ita wannan computer ta iMac mu ji mene ne dalilin saka wannan harafi a bakin shugabanta na wancan lokacin Steve Jobs.

“iMac ta zamanto kamar aure ne tsakanin fasahar Intaner da kuma computer Macintosh” sannan ya kara da cewar “wannan tsarin mun yishi ne domin abokanan huldar mu su sami alaka mai kyau da kuma samun fasahar Intanet mai sauri a gare su”.

Saboda haka babban abin da wannan harafi ke nufi shine ‘Intanet’ a shekarar 1998 wannan shine abi da Steve Jobs ya ce shine ma’anar shi.

Baya da Internet a matsayin ma’anar, haka ya kara da wadansu kalmomi kamar “Inspire” da “Individual” da “Instruct” da kuma “Inform”. Duk da lokacin da kamfanin ya kirkiri na’urar iPod hakika bai taba tunanin intanet a cikin al’amarin ba.

A lokacin da kamfani ya fara yin na’urar kiran waya ta iPhone a shekarar 2007 daya daga cikin abu uku da ya karawa wayar armashi shine maganar samuwar intanet, saboda haka sai dalilin saka harafi ‘i’ sai ya dawo da darajarsa. Sauran abubuwa guda biyun da suka karawa wayar armashi shine kasancewar ana iya kira da ita kuma a saurari sauti duk a wuri guda.

Tun daga wancan lokacin kusan dukkan wata na’ura da kamfanin Apple zai kirkiro sai kaga ya daura mata karamin harafin ‘i’ tare da shi domin dukkan na’urorinsu sai kaga suna baka damar shiga intanet. Sai ya kasance an manta ma’anar harafin sai ya koma ‘i’ na wakiltar dukkan kayan Apple. Dalilin haka ya sanya bayan karbuwar da na’urorin kamfanin Apple su ka yi a kasuwa sai suka yi kokarin cire wannan harafin a wasu sababbin kayansu domin kada sunan kamfanin ya bace. Misali lokacin da suka kirkiro agogo da Talabijin maimakon su kirasu da iWatch ko iTV sai suka canza sunan ya koma Apple Watch da Apple TV.

Duniyar Computer
Salisu Hassan wanda aka fi sani da Salisu Webmaster shine shugaban wannan Muhajja ta Duniyar Computer kuma shugaban kamfanin Duniyar Computer, yana da kwarewa a fannoni da dama na Computer, ya kirkiri shafuka da manhajoji na computer da waya masu yawa, yana da kwarewa a fanni addinin Musulunci, yana jin Turanci da Hausa da Larabci. Magidanci ne kuma yana zaune a garin Kaduna a halin yanzu.

Get in Touch

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Get in Touch

213,390FansLike
25,465FollowersFollow
5,339FollowersFollow

Latest Posts