Manufofin mu

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad (SAW) da iyalan gidansa da Sahabbansa da wadanda suke bin shi da gaskiya har zuwa ranar sakamako.

Wannan Mujalla mai suna Duniyar Computer, mujalla ce da za ta rinka fitowa kowane satin farko a wata. Sannan kuma zata warware dukkannin matsaloli da muke fuskanta ta fannin computer.

Muna da manufofi masu yawa dangane da dalilai na kirkiran wannan mujallar. Kadan daga ciki  sun hada da;

1.      Kaiwa matuka wajen wayar da kan al’umma akan abin da ya shafi Computer. Domin koyarwa da kuma ilmantar da al’umma dangane da abubuwan da suka shafi na’urar, game da matsalolinta da kuma hanyar warware su ta  amfani da bincike, ko kuma tuntubar masana da kwararru a wannan fage.

2.      Wannan mujalla zata rinka amsa tambayoyin masu karatu da kuma amsa waya akan abubuwan da suka shige musu duhu, ta hanyar basu lambobin waya da zasu iya kira kai tsaye ko kuma su aiko da sako na SMS, ko kuma ta hanyar imel.

3.      Zata rinka tsakuro labarai na gida da waje dangane da abubuwan da ya kunshi kimiyya da fasaha.

4.      Shiga makarantun mu domin ganowa da kuma neman warware matsalolin da dalibai da kuma malamai suke fuskanta akan harkar karatun computersu, da kuma taimakawa su daliban wajen warware musu matsalolin da suka fi karfinsu.

5.      Habaka harkar kasuwanci da masu sana’ar sayar da kayayyakin da al’umma suke amfani da su wadanda suka shafi na’ura, ta hanyar sanar dasu wurare da zasu iya samun kayayyaki masu inganci da kuma rahusa.

6.      Sanar da al’ummarmu hali da kuma yanayin da ma’aikatunmu masu alaka da Computer suke, da sanar da mutane ina suka kwana akan harkokin su da kuma in da suka sa gaba.

7.      Tattaunawa da wasu daga cikin al’ummarmu wadanda suka yi fice akan wannan fanni, ko kuma suke taimakawa afannin ilimin  computer, da irin gwagwarmayar da suka yi kafin su kai ga wannan mataki da kuma irin nasarorin da suka samu a rayuwarsu.

8.      Zakulo mashahuran kanfanoni da kuma mutanan da tarihi ba zai manta da suba a fannin computer da kuma fasaha baki daya. Da kuma yin bayani akan wadansu abubuwa da suka shige wa al’umma duhu, ko dai rashin sani, ko kuma sabawa da jin hakan a bakin mutane.

9.      Za kuma mu rinka lekawa  makaratun da ake koyar da ilimin computer wadanda ba shahararru ba, da ma wadanda suka shahara a koyar da fannoni da dama, mu gaya muku irin  kwarewar malamansu,  da kuma yadda suke koyarwa.

10.   Dangane da mashahuran kamfanonin da muke da su na harkar sadarwa, wannan mujalla zata tika tsokaci akan yadda suke gudanar da harkokinsu dangane da abinda ya shafi al’umma, ko dai abinda ya kamata su al’ummar su sani game da kamfanonin, ko kuma abinda kamfanonin suke da bukatar a sanar da al’umma.

11.   Wannan mujalla zata rinka shirya kwasa-kwasai da  da kuma kiran taron karawa juna sani, da kuma shirya tarurruka na bita.akan alamuran yau da kullum wadanda suka shafi computer

Daga karshe mun yi amfani da harshen Hausa da kuma rubutun Hausa saboda al’ummar Hausawa da kuma wadanda suka iya karatu da kuma rubutu, kasancewar wannan ilimi ya bunkasa ta ko wane fanni.

Muna rokon Allah da ya nuna mana gaskiya ya kuma bamu ikon binta, ya cika mana manufofinmu , ya kuma kare wannan mujalla da masu jinta, da masu karanta ta ya kuma daukaki wannan al’umma ya kuma hada kanta, ya bamu daukaka da cigaba a kasar Hausa da duniya baki daya.

Allah ya albarkaci Mujallar Duniyar Computer! Da kasarmu baki daya. Amin