spot_imgspot_img

Yaya Password din ka yake? Yaya kuma ya kamata a ce yake?

Yaya ka ke rubuta password ɗinka a akwatin imel ɗin ka? Ko kuma na facebook ko kuma twitter da duk dai wani shafin internet da kake shiga. Idan har kai ma’abocin ƙoƙarin rubuta lambobi masu sauƙi ne kamar 123456, ko kuma 98654, ko kuma kana amfani da sanannen suna ne wajen password ɗin ka kamar salisu, Ibrahim, ko kuma kai mai son saka sunan masoyiyarka ne kamar Fatima, ko Aisha, ko kuma kai ma’abocin rubutun kalmomin soyayya ne kamar iloveyou, ko kuma fatimamylove ko kuma thankyou, to ina tabbatar da cewar wannan password ɗin naka zai zama mai sauƙi wajen ganowa ko bai zai yi wa hackers wahalar shiga ba domin sa cewa ko kuma aika maka da virus cikin shafukanka ba.

Ga yadda ya kamata ka rubuta password dinka

  • Karanci harrufa goma (10)
  • Ya ƙunshi kananan harrufa da manya a cikin sa
  • Ya ƙunshi alamomin rubutun na musamman
  • Ya kasance akwai lambobi a cikinsu
  • Kada ya ƙunshi sunan masoyi, ko mahaifa da makamantansu
  • Kada ka yi amfani da sanannun kalmomi, kamar iloveyou, ihateyou, ihateu, da makamantansu
  • Kada kuma ka yi amfani da ranar haihuwarka kamar, oct1977.

Ga misali

Dun!yarComput@r98 – Wannan password ya yi ƙarfi sosai.

To, ka yi la’akari idan ka ƙirƙiri password ɗinka da wannan haɗa-haɗe ya kake gani?

Duniyar Computer
Salisu Hassan wanda aka fi sani da Salisu Webmaster shine shugaban wannan Muhajja ta Duniyar Computer kuma shugaban kamfanin Duniyar Computer, yana da kwarewa a fannoni da dama na Computer, ya kirkiri shafuka da manhajoji na computer da waya masu yawa, yana da kwarewa a fanni addinin Musulunci, yana jin Turanci da Hausa da Larabci. Magidanci ne kuma yana zaune a garin Kaduna a halin yanzu.

Get in Touch

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Get in Touch

213,390FansLike
25,465FollowersFollow
5,339FollowersFollow

Latest Posts